Join or Sign In

Sign in to add and modify your software

Continue with Facebook Continue with email

By joining Download.com, you agree to our Terms of Use and acknowledge the data practices in our Privacy Policy.

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) for Android

By uyaapps Free

Developer's Description

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani shahararen marubucin tarihi ya wallafashi da harshen larabci.Shine aka fassara shi zuwa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ilimi akan cikakken tarihin Manzon Allah (S.W.A).

Littafin ya kunshi gundarin rayuwar Manzon Allah tun daga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai, ya kara bamu asali da kuma tarihi na musulunci tun daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa, a takaice shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).

Ina fatan wannan application wanda akayi shi don saukin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.

Don Allah idan har kaji dadin wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.

Takaitaccen tarihin manzon Allah SAW.

Manzo Muhammad Al-Habib an Abdullahi (Sallallahu alaihi wa sallam).

Muhammad an Abdullahi an Abdul-Muallabi an Hashimi an Abdu-Manafi an usayyi an Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abl-Qsim Muammad ibn Abd Allh ibn Abd al-Mualib ibn Hshim ibn Abd Manf ibn Qusayy ibn Kilb) nasabarsa maaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (minah) 'yar Wahbi an Abdu-Manaf an Zuhrata an Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.

Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi xan Akhdabl.

'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Xalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.

Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali xan Abi Xalib (a.s) da Hasan xan Ali da Husain xan Ali da Aliyyu xan Husaini da Muhammad xan Ali da Ja'afar xan Muhammad da Musa xan Ja'afar da Ali xan Musa da Muhammad xan Ali da Ali xan Muhammad da Alhasan xan Ali da Muhammad xan Hasan Mahadi (a.s).

Ayi karatu lfy

Full Specifications

What's new in version 1.0

General

Release May 30, 2019
Date Added May 30, 2019
Version 1.0

Operating Systems

Operating Systems Android
Additional Requirements Requires Android 4.0 and up

Popularity

Total Downloads 46
Downloads Last Week 0
Report Software

Related Apps

Wattpad Free Books

Free
Wattpad Free Books

Moon+ Reader

Free
Moon+ Reader

NOOK: Read eBooks & Magazines

Free
NOOK: Read eBooks & Magazines

Audiobooks from Audible

Free
Audiobooks from Audible

Best VPN Services for 2021

Best for privacy

3 months free with 1-year plan

Best for customer support

$39.99 for the first 12 months

Best for zero logs

$4.87.99/months for a 1-year plan

Best money-back guarantee

$2.99/months for a 3-year plan